Test Footer

Dansanda ya yiwa soja dukan tsiya a wajen na’urar ATM dake DamaturuRundunar yansanda sun tafi da soja tare da dan sanda dan bincike al'amarin da ya janyo rikic ia tsakanin su Wani jami’in yansada ya ji ma wani soja rauni a lokacin da rikici ya barke a tsakinin su a wajen cire kudi a na'urar ATM dake Damaturu.
NAIJ.com ta samu rahoton cewa, rikicin ya fara na lokacin da wani soja ya zo cire kudi daga ATM, ya samu mutane suna bin layin cire kudi, amma shi yaki bi layin.
Mutanen da ke wajen suka nuna masa rashin amincewa akan zarar da yake so ya mu su, daganan wani dansanda dake cikin layin ya tunkari shi ya ce ma sa dole ya bi layi idan lallai yana son ya cire kudi daga na'urar ATM din.
Daganan rikci ya barke a tsakanin su, har suka fara kokuwa da juna, Dansanda ya samu galaba akan soja yayi masa dukan tsiya, har ya jima masa mumunar rauni a jiki. Rundunar yansadar 2ic dake Damaturu sun tafi da dansadar tare sojan dan bincike.
Daga Naijhausa

0 Response to "Dansanda ya yiwa soja dukan tsiya a wajen na’urar ATM dake Damaturu"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel