Test Footer

Duk wanda tace sai na neme ta kafun na sata a fim ta fito ta fallasa ni – inji Adam A Zango- A Zango ya kalubalanci duk wata yarinya data san ya neme ta, ta bayyana ma Duniya Tauraron fina finan Kannywood, Adam A Zango ya kalubalanci duk wata mace daya taba sakawa a cikin fina finansa ta bayyana ma Duniya idan ya taba nemanta da fasikanci kafin ya sanya ta cikin fim.
A Zango ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook, inda yace “Duk Wadda Da Tace Saina Nemeta Kafin In Sakata A Film Ta Fito Gidan Tv Ko Redio Station Ta Fadawa Duniya. Idan Kuma Ta Rufa Min Asiri Allah Ya Tona Mata Nata Asirin.”
Wasu daga cikin matan da suka bayyana ma duniya irin lalatar da aka yi dasu kafin a sanya su cikin fina finai sun hada da Angelina Jolie, Hilarie Burton, Rose McGowan, Cara Delevingne, Kate Beckinsale da sauransu, yayin wadanda ake tuhuma sun hada da Harvey Weinstein, Kevin Spacey, James Toback, Ben Affleck, da Chris Savino.

0 Response to "Duk wanda tace sai na neme ta kafun na sata a fim ta fito ta fallasa ni – inji Adam A Zango"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel