Test Footer

Faransa An Bude Sabon Gidan Abinci Da Mutane Zasu Dinga Zuwa Zigidir(Hotuna)


A kasar Faransa an bude wani sabon gidan abinci da mutane zasu dinga zuwa cin abinci zigidir. Sabon gidan abinci mai suna O’naturel an bude shi ne a babban birnin kasar Faris, sabon gidan abincin zai baiwa dangi da iyalai damar zuwa su yi karin kumallo ko cin abincin rana ko cin abin dare.

An dai bude wannan sabon gidan abincin ne a ranar Juma’ar nan da ta gabata, bayan da masu rajin yawo tsirara sukai ta kiraye kirayen a bude shi, domin suje su gwangwaje tare da iyalansu.
Manajan gidan sabon abincin Mista Stephane Saada, ya bayyana jin dadin kan irin yadda jama’a ke tururwa zigidir suna zuwa domin su ci abinci a wajensu. Yace wannan abin da mutane ke yi ya kara musu kwarin guiwa, kuma zasu zage dantse wajen ganin sun hidimtawa mutane.
Haka nan, suma masu makwabtaka da gidan abincin sun nuna jin dadinsu kan yadda aka bude sabon gidan abincin da zai basu damar zuwa cin abinci da iyalansu zigidir. A wannan gidan abinci, kudin abinci mafi arha shine wanda kudinsa ya kama kudin tarayyar turai (Euro 30) Kimanin Naira 12,420. Jama’a da dama sun bayyana farashin da cewar bai yi tsada ba.
Allah daya gari bamban. Meye ra’ayinku kan wannan batu?

0 Response to "Faransa An Bude Sabon Gidan Abinci Da Mutane Zasu Dinga Zuwa Zigidir(Hotuna)"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel