Test Footer

Gwamnatin tarayya ta fitar da N5.5bn don gyaran zaizayar kasa a jihohi shidaHukumar zartarwa ta yarda da fidda kudin gyaran zaizayar kasa - Ta kuma yarda da fitar da N165mn don inganta irin masara - Ta yarda da yarjejeniyar safara jirgin sama tsakanin Najeriya da Kanada Hukumar zartarwa ta kasa (FEC) ta yarda da fitar da N5.567 bn don gyaran zaizayar kasa a jihohi shida.
Mai bawa shugaban kasa shawara a harkar labarai, Mista Femi Adesina, ne ya fadawa manema labarai a Abuja, tare da ministan harkokin noma, Mista Audu Ogbeh, da ministan harkokin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika.
Adesina ya lissafa jihohi shida da su ribatu da wannan, wanda sun hada da Kano, Bayelsa, Sakkwato, Ondo, Osun, da Inugu. Gwamnati na yin wannan gudunmawar gyaran zaizayar kasar sau hudu a shekara duk bayan wata uku-uku.
Wannan da aka sa hannu na kwata na uku ne na bana (wato watannin Yuli, Agusta da Satumba). Ogbeh ya baiyana cewa kari kuma an yarda da fitar da N165mn don samar da ingantaccen irin masara har tan 30,000 da makarantar binciken noma take yi a jami'ar Ahmadu Bello University, a Zaria.
"Matsalar da ake samu wajen noman masara a kasar nan shine ba'a da ingantaccen iri; saboda haka in aka nome hekta daya ta masara sai ka ga buhunhunan da aka samu basu fi a irga ba."
Ogbeh kuma yayi magana a kan masu satar hanyar shigo da kayan abinci daga kasar waje ta daji, ya ce Najeriya tana yin asara N5bn duk shekara.
A ranar Talata Buhari ya nada Osibanjo shugaban kwamitin da zasu yaki 'yan sumogul din kayan abinci, kuma ya ce duk wanda aka kama sai ya dandana kudar sa.
Sirika kuma ya gayawa manema labarai cewa kwamitin zartarwar ya sa hannu a yarjejeniyar da Najeriya da kasar Kanada ta yi don safarar jirage.

0 Response to "Gwamnatin tarayya ta fitar da N5.5bn don gyaran zaizayar kasa a jihohi shida"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel