Test Footer

Kannywood: Rigima Tsakanin Rahama Sadau Da Jarumi Ali Nuhu Ta Barke


Daga Mikiya Facebook
Binciken da muka yi ya nuna mana cewa tsskanin Magoya bayan Jarumi Ali Nuhu Dana Rahama Sadau suna Ruwan Ashariya Tsakaninsu
su dai magoya bayan Ali Nuhu mohammed suna hakan ne domin zargin jarumar da yi wa ogan na su zagon kasa. anda a ganin su ita jarumar tana yin zagon kasan ne don anki a sanyata a cikin jerin jaruman da za su fito a fim din FKD na gaba mai suna ABOTA, sai aka sanya wadda basu shiri da ita wato Nafisa Abdullahi.
Wata majiya ta tabbatar mana da cewa tuni dai duk wani makusancin Ali Nuhu da mukarrabansa a ka sanyasu su ka yi ‘Unfollowing’ din Rahama Sadau a shafin su Instagram.
Yanzu haka dai magoyan bayan Ali Nuhu sun sanya damarar Rigima da Jarumar a shafukan su na yanar gizo. Ga kadan daga cikin rubututtukan wasu:
“Wallahi duk wanda ya taba Ali Nuhu sai Inda karfina ya kare, an yi walkiya mun ganki Kin manta lokacin da kike cikin wahala aka fito da ke a cikin mutane” Kin manta lokacin da aka fifitaki akan kowa? Kin manta lokacin da wulakantaki shi din da kike Zagi ya rufa maki asiri?
“To, Wallahi ki shiga taitayinki, ki kuka da kanki. Don wallahi muna jiranki sai kin maimaita duk abin da kika fadi. Kuma kin yi kan ki kar ki kara cewa shi babanki ne shi wawuya… KORARRIYA Ga kuma Abunda magoya bayan Rahamar suka Rubuta kamar haka suna cewa dan Allah yai ma ni’ima , ya Daukaka, tilas sae kayi hkuri da wayanda za suyi mk hassada, da sharri dan dae sucinma gurinsu. Kiyi hkuri da ZAGI, BAKAR MAGANA, ko CIN ZARAFI a boye ko a sarari ko ta social media da ake yi. Rahama sadau Karki rama zagi idan an yi miki, domin in baki ramaba mai zagin iyayensa ya zaga. Kisani Idan Jama’a zasu taru domin su amfanar da ke wani abu a duniya, wlh baza su amfanar da ke komai ba sai abin da Allah ya tsara a gareki. Haka da Jama’a zasu hadu domin su cutar da Ke ko suga kin walaqnta wlh baza su iya yin ko daya ba, sai abin da Allah ya tsara a kanki Karki kalli magulmata, Aikinsu suke yi, Ba ke ki ka basu aikin ba ” me zakuce?

0 Response to "Kannywood: Rigima Tsakanin Rahama Sadau Da Jarumi Ali Nuhu Ta Barke"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel