Test Footer

Kasafin Kudi 2018: Bangaren ayyukan raya kasa ya sami kaso mafi tsoka


Najeriya ta bayyana kasafin kudinta na 2018, wanda gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ke fatan zai samar da yanayin cigaba daga halin karayar tattalin arzikin da take fama da shi. Shugaba Buhari ya bayyana kasafin kudi na Naira tiriliyan 8.6 a gaban majalisar kasar, wanda ya ce zai samar da ayyukan yi ga matasa da kuma sabbin gine-gine a kasar.
A bana ne Najeriya ta fita daga matsalolin koma-bayan tattalin arziki bayan faduwar farashin man fetur, a shekarun baya-bayan nan.
A jawabin da ya gabatar, shugaba Buhari ya ce Najeriya: "ba za ta yi sakacin komawa cikin rikice-rikicen da suka addabi kasar a shekarun baya a yankin Neja Delta mai arzikin man fetur ba.
Kasafin na bana ya zarce na bara da karin kaso 16 kuma gwamnatin Najeriya ta ce za ta mai da hankali wajen samar da hanyoyi da kiwon lafiya da gidaje da kuma samar da ayyukan yi.
Jadawalin manyan ma'aikatun da suka samu kaso ma fi yawa a wannnan kasafin kudin na 2018 ya nuna cewa ayyuka raya kasa

A karkashin kasafin kudin na bana, ma'aikatar Wutar Lantarki, Ayyuka da Gidaje ce ta sami kaso ma fi tsoka na Naira biliyan 555.88. Shugaba Buhari ya bayyana dalilin ba wannan ma'aikata kaso mai yawa: "Gwamnati na son samar da sabbin ayyuka da zsu kawo cigaban tattalin arziki da raya kasa.
Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ce ke ta biyu, inda aka ware mata Naira biliyan 510.87, daga nan sai ma'aikatar Ilimi da zata sami Naira biliyan 435.01.
Daga nan kumasai ma'aikatar Tsaro da zata sami Naira biliyan 422.43, sai ma'aikatar Kiwon Lafiya da aka ware mata Naira biliyan 269.34.
Ma'akatar Sufuri an ware mata Naira biliyan 263.10, inda aka ba ma'aikatar Noma da Raya Karkara Naira biliyan 118.98. Sai kuma ma'aikatar Albarkatun Ruwa da zata sami Naira biliyan 95.11, sai kuma ma'aikatar Ma'aikatu da Cinikayya da Zuba Jari mai kason Naira biliyan 82.92 Amma ana sa ran gibin dake tsakanin kasafin kudin shiga da ainihin wadanda zasu shiga lalitar gwamnati zai ragu daga Naira tiriliyan 2.005 wanda raguwa ce idan aka auna da na bara wanda ya kai naira triliyan 2.36. Kasafin kudin dai zama doka ne kawai idan 'yan majalisar kasar suka amince da shi. Bangaren gwamnati da na majalisa sun sha kai ruwa rana kan kasafin kudi musamman wanda ya gabata, al'amarin da har ya kai ga tonon silili tsakanin 'yan majalisar.

0 Response to "Kasafin Kudi 2018: Bangaren ayyukan raya kasa ya sami kaso mafi tsoka"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel