Test Footer

Kwankwaso ya yaudari Buhari - Ali BarakatƊaya daga cikin jaoran matasa magoya bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Ambasada Ali Barakat ya bayyana cewa, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi`u Musa Kwankwaso, ya yaudari shugaban Ƙasar da ayyuka dake cike da son zuciya.
Barakat ya bayyana haka ne cikin wata hira da ya yi da wata kafar yaɗa labarai mai zaman kanta a makon da ya gabata a garin Kano. A cewar sa lokacin da suka kai wa Kwankwaso ziyara gidan gwamnati, ƙarƙashin Jagorancin shugaba Buhari basu san ayyukan da gwamnan ya yi na son zuciya ba ne, sai yanzu da suka ga komai a bayyane.
Haka kuma ya ce, Ayyukan da tsohon Gwamnan ya ɗebo a ƙananan hukumomi 44 na gina hanyoyi kilomita biyar a kowacce ƙaramar hukuma ba a yi komai ba, amma ya kwashe kaso mai tsoka a aikin da ya bayar haka aikin Gina makarantun nazarin harshen larabci da Addinin Musulunci shi ma aikin bai yi nisa ba amma Sanata Rabi`u Musa ya kwashi kaso mai tsoka a kuɗin.
Ya dai bayyana cewa akwai maƙudan kuɗaɗe da ya yi awon gaba da su da sunan ya yi aiki saboda haka duk wata Badaƙala yanzu Buhari ya na da cikakken bayani.
Daga ƙarshe Barakat ya jadadda cewa, ko da ace shugaba Buhari bai yi niyyar sake tsayawa takara ba a 2019 zasu tursasa masa ya yi hakan kamar yadda suka yi a baya, don ya ɗora akan inda ya tsaya na gyaran Najeriya, kuma ya ce bai kamata Kwankwaso ya matsu da sai ya zama shugaban ƙasa ba a wannan lokaci, ya jira tukunna har lokacinsa.

0 Response to "Kwankwaso ya yaudari Buhari - Ali Barakat"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel