Test Footer

Mahaifiyata Ta Yi Min Addu’ar Samun Nasara A Sana’ar KaruwanciWata ‘yar shekara 18 da rundunar Rapid respond squad ta kama a jihar Legas yayin da take neman fita kasar waje ta shaida cewa da goyon bayan mahaifiyarta wajen fitar ta kasar domin yin aikin karuwanci.
An dai kama Elo Etim ne tare da wata Frances Bamidele tare da jagoran su wanda ta jawo kansu ga aikin Martha Edea yayin da suke neman fita zuwa Abidjan babban birnin tarayyar kasar Ivory coast.
Da take bada amsar tambayoyi Etim tace: “Na san cewa Madam Martha zata tafi damu kasar waje domin yin aikin karuwanci kuma mahaifiya ta tana sane da haka itama Ta bani kudi ma kuma tana mai cewa da in ba yara kanana dake unguwa gwara in tafi inyi kudi da jikina tare da tura mata kudin kashewa.
Tayi min addu’ar samun nasara a sana’ar kuma ta yarda nayi aikin”. Jagoran tafiya kuma shahararar mai safara da mutune zuwa kasashen waje domin aikin karuwanci Martha Edea ta sanar cewa itama ta dade tana harkar karuwanci a Abidjan kuma bayan ta biya bashi dake kanta ta samu yancin daga uwargidan ta wanda ta kaita kasar. Bayan ta samu yanci ne ta fara safarar mata zuwa kasar domin itama ta samu kudi.
Yayin da jami’an RRS ke bincike a cikin jakar ta sun gano wasu kayan shafe-shafe biyu wanda ta shaida masu cewa tsibbu ne wanda ke taimakawa wajen samun farin jini daga mazaje da kuma kariya daga miyagun yanayi. Jami’an dai sun mika su ga hukumar dake lura da masu safarar mutane zuwa kasashen waje ta NAPTIP.

0 Response to "Mahaifiyata Ta Yi Min Addu’ar Samun Nasara A Sana’ar Karuwanci"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel