Test Footer

Mambobi 500 na jam'iyyun PDP da ANPP sun sauya sheka zuwa APC a jihar EkitiA ranar Alhamis din da ta gabata fiye da mambobi 500 na jam'iyyun PDP da ANPP sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a yankin Afao dake jihar Ekiti domin goyon bayan wani mai neman takarar gwamnan jihar, Mista Kola Alabi.
Wannan daruruwan mutanen sun yi sauyin shekar ne sakamakon irin kyautatawa da kuma irin dawainiya da al'ummar yankin na Afao da Mista Alabi ke yi, wanda suke yi mishi kyawun zato idan har ya zamto gwamnan jihar.
Sun kuma yiwa jam'iyyar APC shaidar jam'iyya ce mai bin ra'ayoyin da kuma inganta zamantakewa da rayukan al'umma, wanda kuma wannan jam'iyya ta kere sauran jam'iyyu akan irin tanadi da ta shirywa al'ummar jihar idan har ta lashe zaben jihar.
Yayin gabatar da jawabai a taron sauyin shekar, Mista Tope Agbanigo wanda shine tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP reshen yankin Afao ya bayyana cewa, Alabi mutum wanda babu tantamar ingancin shugabancin sa.
A na shi jawabin Alabi ya bayyana cewa, ya na mutunta tsarin shugabancin jam'iyyar APC karkashin jagorancin Asiwaju Bola Tinubu wajen tantance dan takara na gari da zai yi nasara akan jam'iyyar PDP a zaben gwamnoni na shekarar 2018 mai gabatowa.

0 Response to "Mambobi 500 na jam'iyyun PDP da ANPP sun sauya sheka zuwa APC a jihar Ekiti"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel