Test Footer

Mun ƙwato naira biliyan 738.9 cikin shekaru biyu kacal – Ibrahim MaguShugaban hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta bayyana adadin kudin data kwato daga hannun barayin gwamnati cikin shekaru biyu da suka gabata.
Shugaban hukumar, Ibrahim Magu ne ya bayyana haka a ranar Laraba, 8 ga watan Nuwamba, a birnin Vienna, na kasar Austria inda ake gudanar da taron majalisar dinkin duniya akan cin hanci da rashawa.
Magu yace daga watan Mayun 2015 zuwa Oktoban 2017, sun kwato dala biliyan 2.9, kwatankwacin naira biliyan 738.9 kenan, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Kaakakin EFCC, Wilson Uwaujaren ya bayyana yadda jawabin Magu a taron ya kasance, inda ya gabatar da kasida mai taken ‘Hadin kan kasashen duniya wajen tallafin ilimin kimiyya; abinda Najeriya ta fuskanta.’ Magu yace sun yi amfani da hanyar bani gishiri, in baka manda, inda barawo zai dawo da kudaden daya sata, ba tare da an kai shi kotu ba, “A shekarar nan kadai sun kwace kadarori da suka kai biliyoyin nairori. “Sun haa da dala miliyan 43, da naira biliyan 2 na tsohuwar minista Diezani Alison, wanda ta sata daga kudaden albashin Yansanda, dake ajiye cikin asusun banki guda bakwai a bankuna uku.” Inji Magu. Haka zalika yace ana samun cigaba tare da taimakon kasashen waje don maido ma Najeriya kudaden da Abacha ya sata da kuma kudin makamai.
Daga karshe ya bukaci da a rage tsayin lokacin mayar ma kasashe masu tasowa kudaden sata da aka jibge su a kasashen Duniya, sa’annan ya shawarci mahalarta taron da a dinga hukunta duk wani banki daya karya dokokin satar kudi.

0 Response to "Mun ƙwato naira biliyan 738.9 cikin shekaru biyu kacal – Ibrahim Magu"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel