Test Footer

Nigeria: Wata sabuwar cuta ta 'kashe' yara 50 a JigawaRahotanni daga jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya sun ce a kalla yara 50 ne suka mutu a kauyen Gidan Dugus da ke karamar hukumar Dutse, sakamakon bullar wata cuta da ba a gane ta ba.
Wasu kafafen yada labarai na yankin sun ce yaran sun mutu ne cikin makonni hudu zuwa biyar da suka gabata.
Wani dan jarida da ke yankin ya shaida wa BBC cewa dagacin kauyen da al'amarin ya faru, ya tabbatar masa da faruwar lamarin. Ya ce yaran da suka mutun duk sun fito daga kauyen na Gidan Dugus, wanda ke da nisan kilomita 35 daga Dutse babban birnin jihar, kuma dukkansu suna tsakanin shekaru biyu ne zuwa shekaru biyar.
Kawo yanzu dai jami'an lafiya na jihar ba su ce komai ba, amma jaridar The Nation ta ambato sakataren ma'aikatar lafiya na jihar Alhaji Ali Dandidi, yana cewa cutar ta bulla ne tun a watan Yuli.
"Tun a wancan lokacin al'ummar yankin suka ki zuwa cibiyar lafiya. Sai suke ta sayen magani daga kemis da sauran wurare." "Tun bayan da aka sanar da hukumomin lafiya a watan Oktoba suka yi kokarin shawo kan matsalar, suka kuma maganceta bayan gano cewa zazzabin maleriya ne da na taifod yaran suka yi fama da su, in ji Alhaji Ali Dandidi.
Sai dai duk da wannan ikirari na Alhaji Dandidi, mazauna yankin sun tabbatarwa da BBC cewa har yanzu ana fama da wanann cuta ana kuma ci gaba da samun mace-macen. Sun kuma ce ba a kai ga gano ainihin wacce irin cuta ba ce.
Wasu rahotannin sun ce a gida daya ana iya samun yara hudu zuwa shida sun mutu duk sakamakon cutar.

0 Response to "Nigeria: Wata sabuwar cuta ta 'kashe' yara 50 a Jigawa"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel