Test Footer

Paradise Papers: An ambato Saraki cikin masu kauce wa harajiSunan Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki, ya fito cikin jerin sunayen attajiran da suke kauce wa biyan haraji da aka kwarmata da aka yi wa lakabi da Paradise Papers.
An tsaigunta bayanan ne ga jaridar Sueddeutsche Zeitung ta Jamus, wacce ta bai wa kungiyar 'yan jarida masu bincike ta kasa da kasa (ICIJ) ciki har da BBC da jaridar Premium Times ta Najeriya.
Premium Times ta wallafa Bukola Saraki, wanda shi ne mutum na uku mafi girman mukami a tsarin siyasar Najeriya, ya kafa kamfanin Tenia Limited a tsibirin Cayman Islands a shekarar 2001.
Kuma ya ci gaba da zama daraktan kamfanin da kuma mamallakinsa har zuwa shekarar 2015. Tsibirin Cayman Islands dai ya shahara wajen boye kadadarorin wadanda ba sa san biyan haraji.
Mai magana da yawun Saraki Yusuph Olaniyonu ya shaida wa BBC cewa suna nazari kan bayanan kuma za su bayyanar matsayarsu nan gaba. Sai dai wani lauya da ke wakiltar Sanatan wanda ke zaune a Birtaniya, ya tabbatar da cewa kamfanin nasa ne, amma ya ce "babu wata doka da aka karya."
Kamar sauran 'yan siyasar duniya da sunansu ya fito a katardun Paradise Papers, wadannan bayanai ba za su yi wa Sanata Saraki dadin ji ba ganin yadda yake sahun gaba wurin kiraye-kirayen a kawo sauyi domin inganta tsarin karbar haraji a kasar.
Jaridar Premium Times ta ambato wani jami'i a kamfanin lauyoyi da ke wakiltar Saraki, Andrew Stephenson, yana tabbatar da cewa Tenia Limited kamfanin shugaban majalisar dattawan Najeriyar ne. Sai dai kuma jami'in ya wanke shi daga aikata ba daidai ba.
A martaninsa ga tambayar da kungiyar ICIJ ta yi masa, Mista Stephenson ya ce: "Babu wani laifi a mallakar kamfanoni a kasar waje," kuma ya kara da cewa kamfanin bai taba aiki ba tun da aka kafa shi.
Ya ce: "An sanar da mu cewa Tenia Ltd bai taba mallakar wata kadara ba, bai yi ciniki ko kuma wani kasuwanci ba, kuma ba shi da alaka da zaman kotu [shari'ar da ake yi wa Saraki] a Najeriya."
Bayanan Panama Papers
Sunan mai dakin Bukola Sarakai da wani na kusa da shi sun bayyana a lokacin da aka kwarmata bayanan jerin sunayen masu kauce wa biyan haraji na Panama Papers da kungiyar ICIJ ta jagoranta a shekarar 2016.
Sai dai a watan Nuwamban bara ya shaida wa Editan BBC na Abuja, Naziru Mika'ilu, cewa "batu ne na kafa kamfani, ba na kauce wa biyan haraji ba".
Da aka tambaye shi kan dalilin da ya sa aka kafa kamfanin, sai ya ce: "An yi hakan ne bisa shawarwarin lauyoyi, saboda za a sayi wata kadara, kuma ita ce shawarar da aka bayar a wancan lokacin." Ya ci gaba da cewa: "Ba wai kamfani ne da muka kafa da kanmu ba, a'a, lauyoyi ne suka kafa, kuma a iya saninmu babu wata doka da aka keta."
'Karya wurin bayyana kadarori' Ba ya ga haka, Saraki yana fuskantar tuhuma kan zargin yin karya wuirn bayyana kadarorinsa, amma ya bayyana tuhumar a matsayin bita-da-kullin siyasa.
Daga baya dai kotun da'ar ma'aikata ta kasar ta wanke shi daga zargin, amma kuma gwamnatin tarayya ta daukaka kara.
Babu tabbas ko tasirin da wannan rahoton na baya-bayan nan ka iya yi a fagen siyasar kasar.
Amma wasu masu sharhi na ganin zai iya sa wa a mayar da hankali kan yadda 'yan siyasar ke gudanar da al'amuransu musamman wadanda suka shafi harkokin kasuwanci da kudi.
Gwamnatin Shugaba Buhari dai ta zo kan mulki ne da alkawarin yakar cin hanci da rashawa da inganta tattalin arzikin kasar.

0 Response to "Paradise Papers: An ambato Saraki cikin masu kauce wa haraji"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel