Test Footer

Ranar Da Moppan Tasa Zata Dawo Da Rahama Sadau Kannywood

r" style="text-align: left;" trbidi="on">

A ranar wannan Larabar ne ake sa ran cewa uwar kungiyar masu shirya finafinan Hausa ta Nijeriya, wato MOPPAN, za ta d’age takunkumin da ta kakaba wa jaruma Rahama Sadau shekara daya da ta gabata.
Wata majiya ta shaida wa mujallar Fim cewa a ranar ne shugabannin kungiyar za su yi wani zama na musamman inda za su tattauna batun rokon gafara da jarumar ta yi a makon jiya, “kuma akwai tabbacin za a yafe mata.”
Majiyar ta ce tun a ranar Alhamis da ta gabata ne kungiyar ta so ta yi mitin a kan maganar, to amma hakan bai samu ba saboda shugaban kungiyar, Alhaji Kabiru Maikaba, ya na fama da ciwon kunne.
Saboda haka ne sauran shugabannin su ka zauna ran Asabar, inda su ka duba batun bada hakuri da jarumar ta yi. Idan kun tuna, an kori Rahama Sadau daga Kannywood ne a farkon watan Oktoba na 2016 sakamakon bullar wani bidiyo na rawa da waka da ta yi da wani mawakin hip-hop mai suna ClassiQ, inda aka gan su su na rungume-rungume.
Hakan ya harzuka shugabannin MOPPAN din wadanda su ka bada sanarwar korar ta daga masana’antar shirya finafinan saboda a cewar su abin da ta aikata ya saba wa addinin Musulunci da kyawawan al’adun Hausawa.
‘Yan fim din Hausa su na shan suka daga wani sashe na jama’a masu ganin cewa irin finafinan da ake yi ba su dace da rayuwar malam Bahaushe ba. Sukar kuma ta kan shafi rayuwar ‘yan fim din.
Kungiyar MOPPAN ta dukufa wajen ganin ta saisaita zaman ’ya’yan ta, musamman jarumai wadanda su ne aka fi sani.
Mujallar Fim ta smau labarin cewa a zaman da shugabannin MOPPAN din su ka yi a ran Asabar, akwai wadanda ba su goyi bayan a yafe wa jarumar ba saboda, a cewar su, sam ba ta yi nadama ba a lokacin da ta aikata wancan abin da su ke ganin laifi ne.
Amma yawanci sun ce ya kamata a hakura kawai tunda dai yanzu ta kawo kan ta, “don a wuce wajen kawai.” Majiyar mujallar Fim ta ce duk da yake za a yafe wa jarumar, amma kuma za a kafa mata sharudda wadanda idan ta amince da su ne za a janye korar da aka yi mata.
Sharuddan sun hada da cewa daga yanzu kada ta kara aikata wani laifi a masana’antar Kannywood kamar yadda ta yi a baya, misali rawa da ba ta dace ba da kuma bayyanar da jikin ta duniya ta gani.
Ita dai Rahama Sadau, bayan korar ta daga Kannywood sai ta tsunduma harkar finafinan Kudu na ‘yan Nollywood da kuma daukar hotunan kwalliya irin na ‘yan Kudu din. A baya, ba ta bayyana nadama ba kan korar ta daga Kannywood da aka yi domin da alama ta na ganin cewa tauraruwar ta ma ta kara haske bayan korar tata.
A wata hira da aka yi da ita a jaridar The Guardian kwanan nan, Rahama t ace yaznu duniya ta kara sanin ta sakamakon korar ta da aka yi daga Kannywood.
Wani masanin harkar Kannywood ya shaida wa mujallar Fim cewa, “Yanzu ta ga uwar bari ne, ta ga cewar duk inda ta je ta dawo dai sunan ta ’yar Kannywood.
Sannan kuma wani abu da yawanci ba a sani ba shi ne duk kudin da ta ke samu a Nollywood bai kai wanda ta samu a Kannywood ba inda a kullum cikin aiki ta ke.” Fitaccen jarumi Ali Nuhu dai shi ne ya jagoranci Rahama wajen bada hakurin a Kano a makon jiya, inda su ka ziyarci Hukumar Tace Finafinai, da gidajen rediyo da kuma shugabannin MOPPAN.
Rahama Sadau ta mika takarda ga MOPPAN din inda ta ba kungiyar hakuri kan abin da ya faru, kuma ta sha alwashin cewa ba za ta kara aikata wani abin assha ba.

0 Response to "Ranar Da Moppan Tasa Zata Dawo Da Rahama Sadau Kannywood"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel