Test Footer

Shahararren dan kasuwar nan Aliko Dangote yayi kyautar Dala miliyan 100Shahararren dan kasuwar nan dan asalin jihar Kano dake a arewacin Najeriya mai suna Alhaji Aliko Dangote ya yayi alkawarin bayar da gudummuwar dalar Amurka miliyan 100 a cikin shekaru akalla 5 a karkashin gidauniyar sa domin magance matsalar yunwa a Najeriya.
Gidauniyar ta Dangote ce dai tayi sha wannan alwashin a kwanan bayan yayin da ake kammala wani muhimmin taro game da matsalar yunwa da rashin abinci mai gina jiki da aka gudanar a garin Milan, kasar Italiya.
Majiyarmu dai ta samu cewa tarin dai na zaman irin sa na biyu da aka gudanar tun bayan da kaddamar da wani tsari na shekaru goma da zai taimaka wajen kawo karshen matsalar yunwar a duniya da ke da goyon bayan kasashe da dama da kuma kungiyoyin sa kai.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa hamshakin mai kudin ma a kwanan baya ya taimaka wa al'ummar fulani da rikicin tsaunin Mambila ya rutsa da su da kudaden tallafi domin rage radadin wahalhalun su.

0 Response to "Shahararren dan kasuwar nan Aliko Dangote yayi kyautar Dala miliyan 100"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel