Test Footer

TAURARIN NISHAƊI: Haƙuri Ya Zama Jarina A Harkar Fim – ZulaihatA duk lokacin da aka duba masana’antar finafinai ta Kannywood za a ga fuskokin jarumai masu yawa da suke gudanar da harkokin sana’ar su a cikinta.
ZULAIHAT UMAR tana ɗaya daga cikin jarumai mata da suke ba da tasu gudunmuwar a wannan lokacin kuma za a iya cewa jarumar tana cikin sahun mata masu aji duk da cewar ba ta kai matakin manyan jarumai ba, amma kasancewarta mai iya mu’amala da jama’a ne ya sa jarumar ta yi wa sauran jarumai mata zarra. Ta yi finafinai sama da guda ashirin duk da ba wani lokaci mai tsayi ta ɗauka a cikin masa’antar ba.
Domin jin ko wace ce Zulaihat Umar, wakilinmu ya tattauna da ita. Ku biyo mu ku ji yadda ta kasance: Da farko za mu so ki gabatar da kanki ga masu karatunmu…
To ni dai sunana Zulaihar Umr, kuma ni haifaffiyar arin Kano ce. An haife ni a unguwar Kwandila Zaria Road, kuma na yi karatuna na firamare da na sakandire bayan na gama sai aka yi min aure.
To bayan wasu ‘yan shekaru da yin aurena sai Allah ya kawo rabuwarmu da mijina, sai aurena ya mutu. To wannan dai shi ne kaɗan daga cikin tarihina zuwa yanzu da na samu kaina cikin harkar fim.
Ta yaya aka yi kika samu kanki a cikin harkar fim bayan mutuwar aurenki?
E, bayan mutuwar aurena na yi niyyar shiga harkar fim ne saboda ganin yadda rayuwa take, ina buƙatar na samu wata sana’a da za ta riƙe ni saboda ka san ko da iyaye za su yi maka wani abu to a matsayina na wadda ta mallaki hankalinta to ni in da hali wajibi ne na ɗauki nauyinsu, don haka ganin ba ni da wani jari da zan kama wata sana’a sai na yanke shawarar bari na fara da fim don na ɗan rinƙa samun abin da zan rufa wa kaina asiri kuma daman ina da sha’awar yin harkar. To ka ji yadda aka yi na samu kaina a cikin harkar.
A ƙalla shekarunki nawa a cikin harkar fim a yanzu?
To, shekaruna da na yi da a yanzu ina ganin shekara ta uku kenan.
Ko za ki iya faɗa mana finafinan da kika fara yi na farko?
E, fim ɗina da na fara yi shi ne ‘Jaririna’. Sai kuma fim ɗin kwaɗayi da buri na furodusa Abba Abubakar Babaye. Sai fim ɗin ‘Tashe’, ‘Kasuwanci’, suna dai da yawa don ba zan iya ƙidaya guda ashirin ɗin ba.
Lokacin da za ki fara a matsayinki na sabuwar jaruma, a ya ya kika samu kanki?
E, gaskiya ba zan manta ba, lokacin da na fara wani fim ne mai dogon zango wato “Series” na Darakta Ahmad Bifa. To lokacin sai na kasa yin abin da aka ba ni, amma daga baya sai na nutsu na ci gaba na rinƙa yin abin da ake ba ni umarni a kansa.
Yanzu za a iya cewa kin zama ‘yar gari a cikin harkar idan kika kalli baya kafin ki shiga yadda ake faɗar harkar, ko ya ya bambancin su yake?
Akwai bambanci sosai, domin kuwa yadda harkar fim take daban da yadda ake faɗarta. Don kuwa mutanen da ba su gan ta ba sai ka ji suna cewa ai harkar ba sana’a ba ce kuma ana faɗar maganganu da dama a kan ta. Amma ni dai da na shigo sai na ga abin ba haka ba ne don gaskiya harkar fim sana’a ce kuma abin da ya kamata jama’a su sani duk harkar funiya za ka samu na kirki da na banza, to ka ga ba zai yiwu ba a rinƙa yi wa mutane kuɗin goro.
Wanne irin mataki mace take bi don ta zama cikakkiyar jaruma?
To duk da yake ni ban kai matsayin babbar jaruma ba, abin da na sani shi ne, mace ta riƙe mutuncinta ta zama mai kula da aikin da aka ba ta sannan ta yi haƙuri, juriya a kan abin da ta sa a gaba. Wannan zai sa a rinƙa kallon mace a matsayin mai mutunci da za a rinƙa yin aiki da ita har ta zama jaruma.
Kafin ki kai ga wannan matsayin, ko akwai wasu matsaloli da kika fuskanta?
To, ai ba za a rasa ba. Kaɗan daga cikin matsalolin da na rinƙa samu shi ne idan za a kira ka aiki sai a duba a ga ai kai ba ka kai wani matsayi ba, duk da cewar an duba an ga ka cancanta, amma dai sai a rinƙa kallon ba ka da matsayin sai an yi maka magana daga baya a canza da wani a rinƙa cewa da kai sai gobe, sai jibi da haka har a gama. To irin wannan matsalolin na sha fuskantar su. Amma dai abin alfahari a gare ni irin wannan haƙurin da na rinƙa yi shi ne ya sa kuma daga baya wasu suka gani suke ta kira na aikinsu. A yanzu mutane da yawa ma suna son su yi min fim saboda sun ga yadda na kasance a baya da kuma irin haƙurin da na yi.
Ana ganin harkar fim kamar aktin aiki ne da ba shi da wata wahala, a matsayinki na jaruma, yaya kike kallon maganar?
To gaskiya ba haka ba ne, mutane ne dai suke yi mata kallon hakan. Don haka ne ma idan irin waɗannan mutane suka halarci wajen aikin fim ɗin sai ka ji suna cewa daman haka abin yake da wahala? Domin aiki ne mai cin lokaci da cajin ƙwaƙwalawa, don haka ba abu ne mai sauƙi ba.
Wanne irin buri kike so ki cinma a harkar fim?
Burin da nake so na cimma dai bai wuce na samarwa kaina abin rufin asiri da ‘yan’uwana da iyayena ba. Kuma alhamdulillahi, ina samun nasara ina ganin nan gaba kaɗan burina zai cika. Sannan kuma ɗaya burin da nake da shi ina so na zama fitacciyar jaruma wadda za a rinƙa faɗarta a duniya. Idan har na samu zan yi alfahari da hakan.
Baya ga harkar fim, ko kina wata sana’a ko kasuwanci?
E haka ne, ka ga bayan aktin ina yin waƙoƙi ma na ‘yan siyasa, domin kuwa a yanzu na yi waƙoƙi da dama kuma ina kan yin wasu a yanzu. Sannan kuma ina yin sana’ar haɗa turaruka na amare da gyaran jikin amarya don gari-gari ma ana kira na. Kai ma ina fatan idan ka tashi yin ƙarin aure za ka kira ni gyaran jikin amaryarka. Ko na haɗa mata kayan ƙamshion ɗaki duk ina yin su. Sannan kuma ina yin ɗinki kuma nan gaba kaɗan idan na samu jari akwai finafinan da zan yi furodusin ɗin su.
A yanzu da kika fara shahara ko ya ya kike fama da mutane musamman idan kina tafiya a kan hanya?
To gaskiya ana samun masoya sosai waɗanda suke yaba abin da ka yi a cikin fim su rinƙa yi maka godiya, amma abin da ya fi damu na shi ne idan na je aiki na dawo wani lokacin sai na haɗu da wasu da su ba son harkar suke yi ba. To idan kika kai dare kamar sha biyu zuwa sama duk da kana da katin shaida da za ka nuna ga daga inda kake, to idan ka shigo unguwar sai ka ga ana yi maka wani kallo kamar ka dawo daga harkar banza, alhali daga wajen aiki kake. To, gaskiya wannan yana damuna.
Daga ƙarshe wanne kira za ki yi ga jama’a?
Ni kiran da zan yi shi ne jama’a su rinƙa kyautatawa ‘yan fim zato, ba wai su rinƙa yi musu wani irin kallo ba. Muna yin sana’a ne kuma akwai masu kiyaye mutunci da yawa a cikinmu. Don haka ba a taru an zama ɗaya ba. To madalla mun gode. Ni ma na gode.

0 Response to "TAURARIN NISHAƊI: Haƙuri Ya Zama Jarina A Harkar Fim – Zulaihat"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel