Test Footer

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo ta gindaya wa shugaba Buhari sharadi mai tsauri


Kungiyar kabilar Ibo ta INC (Igbo National Council), ta gindayawa shugaban kasa Muhammadu Buhari sharadi mai tsauri sakamakon zaben 2019 mai gabatowa . Kungiyar ta gindayawa shugaban kasa sharadi da cewar, in har yana son goyon bayan su a zaben 2019 to sai ya sauya kujerar da mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo yake kai a yanzu da wani dan kabilar su na yankin Kudu maso Gabashin kasar nan.
Naij ta fahimci wannan sharadi ya zo ne bayan da shugaba Buhari ya yanke shawarar ziyartar jihohin Kudu maso gabashin kasar a makonnin da suka gabata.
A wani rahoto da sanadin shugaban kungiyar Chilos Godsent da ya bayyana a birnin Owerri na jihar Imo, ya ce wannan ita kadai ce hanyar da jam'iyyar APC za ta samu goyon bayan su a zaben kasa na 2019. Godsent ya kara da cewa, jam'iyyar APC ta maishe da yankin na su saniyar ware wajen gudanar da shugabancin ta a kasar.
Source :- Naijhausa

0 Response to "Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo ta gindaya wa shugaba Buhari sharadi mai tsauri"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel