Test Footer

Dalilin Da Ya Sa Na Karbi Addinin Musulunci – Jarumar Nollywood, Liz AnjorinAn dade ana jjita jita game da dalilin daya sa jarumar Nollywood, Liz Anjorin ta karbi addinin musulunci inda wasu daga cikin masoyanta ke ganin cewa namiji ne ya sa ta sauya.
Jarumar ta fito ta musanta wannan batu tare da bayyana asalin dalilin daya sa ta bar addinin kiristanci ta koma musulunci.
A wani sako da ta wallafa a shafin ta na Instagram, jarumar ta ce mahaifiyar ta musulma ce kafin ta auri kirista, a don haka a lokacin da ta rasu, kowani coci da aka kai ta suka ki karbar ta.
Anjorin ta ce sun kai ta sama da cocina 10, kuma kowanne ya ki yarda ya binne ta. Ta ce a cikin wannan Ibtila’i, mabiya addinin da ta ki, wato msuslunci su suka taimaka mata suka yi wa gawar mahaifiyarta addu’a, suka yi mata sutura, yayin da cocin kawai gurin binne ta suka bayar bayan sun sanya masu wasu ka’doji da ba ta bayyana ba.
Ta ce bayan haka ne ta karbi addinin musulunci, inda har ta tafi aikin Hajj.

0 Response to "Dalilin Da Ya Sa Na Karbi Addinin Musulunci – Jarumar Nollywood, Liz Anjorin"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel